Rikicin Atiku Abubakar Da Wasu Gwamnonin Jam'iyyar PDP Babbar Barazana Ce A Gare Shi

Kannywood Family
2 minute read
0
Rikicin Atiku Abubakar Da Wasu Gwamnonin Jam'iyyar PDP Babbar Barazana Ce A Gare Shi
Rubutawa ✍️ Comr Abba Sani Pantami Duk wanda yake tunanin rikicin Atiku Abubakar da wasu gwamnonin PDP ba kalubale bane ga takarar Atiku ba, to gaskiya ina tunanin baisan siyasar Najeriya ba. A yanzu haka Atiku ya samu matsala na fadan cikin gida tsakanin shi da wasu daga cikin gwamnonin jam'iyyar shi ta PDP da suka hada da; 1, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas. 2, Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu. 3, Gwamna Okezie Ikpeazu na Abia. 4, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe. 5, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo. Yanzu kuma ga Gwamnan jihar Bauchi duk da naga wasu suna cewa an dinke barakar da ta kunno a tsakanin su. Rikicin Atiku da gwamnoni, wasu na ganin kamar fadan yana nema ya zama na kabilanci musamman idan akayi la'akari da maganganun da Gwamnan jihar Benue yayi akan Atiku. Duk wanda yake bibiyar siyasar Najeriya yasan irin tasirin da jam'iyya take dashi a jihar da Gwamna dan jam'iyyar ke mulki, jam'iyya tana matukar samun kuri'u masu yawa a zabe koda ba'a son jam'iyyar, wani lokacin har lashe zabe akan yi saboda Gwamnan jihar yakan yi amfani da karfin mulki, da kudi da amfani da masu fada aji a jiha har a samu nasara. Yawanci idan Gwamnan jiha yana son dan takarar shugaban kasa shi yasan hanyoyin da yake bi na ganin ya tarawa dan takarar shi kuri'u masu tarin yawa koda kuwa ba'a son dan takarar, munga misali masu yawa tun daga zaben 2011, da zaben 2015 da na 2019 a wasu daga cikin jihohin Najeriya. Masu ganin wannan rikicin ba babbar illa bace ga Atiku Abubakar shin ko sun manta da cewa jihohin da jam'iyyar PDP take mulki ba su kai adadin yawan jihohin da jam'iyyar APC take mulki ba? Shin idan har gwamnoni 5 daga cikin jihohin da PDP take mulka kuma jihohin da kowane zabe PDP take yin Nasara suka juyawa Atiku baya suka ki mishi aiki a jihohin su, yaya kuke tunanin sakamakon zai kasance? Yaya kuma kuke tunani idan har gwamnonin jam'iyyar APC suka yiwa dan takarar su aiki da gaske yadda sakamakon jihohin su zai kasance? Ni ba farin ciki ko bakin cikin fadan su nike yi ba, munsan da gwamnonin da Atiku da Tinubun duk abu daya ne, ba suda bambanci, duk jirgi daya ne ya dauko su tun tale-tale dama tare muka gansu. In sunga dama su kara hada kansu in sunga dama su cigaba da fadan su, amma na tabbata indai har basu sasanta kansu ba, to har masu ganin cewa a rabu da gwamnonin basu da wani tasiri, to tabbas sai sun dawo daga baya suna cizon tsaya. Yanzu lokacine na kakar siyasa babu wani batun a yaudare mu da maganan kabilanci, Addini, bangaren ci, ina tunanin yanzu kan kowa ya waye. Babban fatanmu da Addu'ar mu shine Allah ya zaba mana shugaba mafi Alkhairi koda kuwa bamu son shi.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)